Jihar Jigawa: Manoma su rungumi sabbin tsare-tsaren da aka bullo da su a bangaren aikin gona

0 163

Gwamnatin jihar Jigawa ta bukaci manoma su rungumi sabbin tsare-tsarenta da ta bullo da su a bangaren aikin gona domin bunkasa samar da abinci da kuma yalwar arziki.

Gwamna Malam Umar Namadi ya yi wannan bukatar lokacin da yake gabatar da sabbin tsare-tsaren bunkasa aikin gona wadda gwamnatinsa ta bullo da shi a dakin taro na gidan gwamnati.

Malam Umar Namadi ya bayyana cewa tsarin zai taimaka wajen samar wa matasa aiyyukan yi da kuma bunkasa samar da abinci.

Gwamanan ya kara da cewa hakan zai kawo sauye-sauye da dama a fannin aikin gona.

Leave a Reply

%d bloggers like this: