Goodluck Jonathan ya shawarci shugaban Kasa Bola Tinubu da ya karfafa tsarin Dimokuradiyya

0 121

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya shawarci shugaban kasa Bola Tinubu, da ya karfafa tsarin dimokuradiyya, domin bai wa ‘yan kasa ‘yancin fadin albarkacin bakinsu ba tare da hatsaniya ba.

Ya yi wannan kiran ne da safiyar yau a wajen wani taron yini guda na bikin cika shekaru ashirin da biyar a dimokuradiyyar Najeriya ba tare da gargada ba, wanda aka gudanar a dakin taro na Banquet dake fadar gwamnatin tarayya Abuja.

Ya kuma bayyana cewa shugaba Tinubu yana da alhakin tabbatar da dorewar shekaru 25 na mulkin dimokuradiyya.

Jonathan ya kara da cewa dole ne ‘yan siyasa da masu fada aji su su kasance ababen koyi, salon gudanar da rayuwarsu ya nuna cewa masu zabe ne suka zabe su kan wannan mukami.

Ya kuma jaddada bukatar tabbatar da cewa duk ‘yan Najeriya sun amfana da rabon dimokuradiyya ba tare da la’akari da matsayin tattalin arziki ko zamantakewa ba. Dr. Jonathan wanda shi ne shugaban taro, a taron wanda mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya halarta, sakataren gwamnatin tarayya, George Akume da sauran baki, ya bayyana bukatar samar da wani tsari na tsarin dimokuradiyya wanda zai ƙarfafa haɗin kan al’umma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: