Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya gargadi Shugaba Buhari dangane da sake shata guraren kiwo a Najeriya

0 126

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto a yau ya gargadi Shugaban Kasa Muhammadu Buhari dangane da sake shata guraren kiwo a kasarnan, inda yace sana’ar kiwo a sarari baza ta kawo cigaba ba, har ga su Fulani makiyaya.

Yace shugaban kasar zai farfadar da guraren kiwo ne kadai a jihoshi ko yankunan da mutanen wajen suke da bukatar hakan.

Tambuwal yayi jawabi a Lagos a lokacin taron jawabai na cika shekara 63 da haihuwa na Richard Akinnola, wani shahararren dan jarida kuma mawallafi, inda ya bayyana cewa lokaci yayi da za a sauya tunani dangane da dabi’ar kiwo a sarari.

A cewarsa, shugaban kasar zai iya sake farfado da guraren kiwo ne kadai a inda mutane suke da bukata. Hakan a cewarsa, zai dakile karuwar rashin tsaro a kasarnan.

Gwamnan ya kuma yi kiran a wayar da kan makiyaya domin dawo dasu bisa turbar cigaban zamani.

Leave a Reply

%d bloggers like this: