Gwamna Badaru ya bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta magance matsalar fataucin mutane a jihar Jigawa

0 80

Gwamnan Jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar ya bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta magance matsalar fataucin mutane a jiharnan.

Gwamnan ya bayar da wannan tabbacin ne a jiya yayin da yake kaddamar da kwamitin yaki da fataucin mutane na jiha a gidan gwamnati da ke Dutse.

Gwamnan Badaru Abubakar wanda ya nuna damuwa kan ayyukan masu safarar mutane ya ce gwamnati za ta yi duk abin da za ta iya don ganin an dena fataucin mutane a jiharnan.

A saboda haka ya yi kira ga rundunar da ke aiki a jihar da ta himmatu wajen magance matsalar musamman a garuruwan da ke kan iyakar kasarnan.

Tun da farko, Babban Darakta na Hukumar Hana Fataucin Mutane ta Kasa wanda Daraktan Shari’a da Gabatar da Kara, Hamisu Hassan Tahir, ya wakilta ya shaida wa Gwamna cewa tun lokacin da aka kafa hukumar, ta ceto mutane dubu 16 da 277 da aka yi fataucinsu.

Ya ce a cikin adadin, dubu 14 da 474 ‘yan Najeriya ne kuma 172 sun fito ne daga jihar Jigawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: