Gwamna Badaru yace ba dan ya samu tallafi daga Muhammadu Buhari ba da tuni ya ajiye mukamin sa

0 125

Gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar yace ba dan ya samu tallafi daga shugaban kasa Muhammadu Buhari ba, da tuni ya tattara kayansa ya sauka daga mukamin gwamna.

Gwamnnan ya sanar da haka a lokacin da ya karbi bakuncin Ministan Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, wanda yake ziyarar aiki zuwa duban tutar Najeriya mafi tsayi a gonar Mallam Alu dake karamar hukumar Birninkudu a jihar Jigawa.

A cewar gwamnan, gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta marawa gwamnatin jihar baya a matakai daban-daban tun bayan kafa gwamnatin APC mai ci.

Tunda farko, ministan labarai, Lai Mohammed, yace bayan ziyartar fadar sarkin Dutse, ya gano dalilin da yasa jihar Jigawa ce mafi zaman lafiya a Najeriya.

Ministan wanda aka bashi takardar izinin zama dan jihar Jigawa, yace sarkin yayi bayanin yadda masarautarsa tare da tallafin gwamnatin jiha, take sasanta rikice-rikicen cikin gida, abinda ya bayyana da jigo wajen dorewar zaman lafiyar jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: