Gwamna Malam Umar Namadi, ya Rantsar da Sabbin Mambobin Dindindin 2 Na Hukumar Kula da Ma’aikatan Jahar
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya rantsar da sabbin mambobin dindindin biyu na Hukumar Kula da Ma’aikatan Jihar, inda ya bukace su da su kasance masu bin ka’ida da gaskiya a yayin gudanar da aikinsu.
Taron rantsuwar ya gudana ne a zauren majalisar gwamnatin jihar da ke Dutse, inda Babandi Saleh da Ibrahim Adamu Fagam suka sha rantsuwar aiki a gaban jami’an gwamnati da manyan baki.
Ya nuna kwarin gwiwa cewa sabbin mambobin, da kwarewarsu da jajircewarsu, za su inganta aiki tare da tabbatar da biyan bukatun al’ummar Jigawa.
A karshe ya taya su murna tare da tunatar da su, su tsaya tsayin daka wajen sauke nauyin da aka dora musu domin ci gaban jihar.