Masarautar Garin Hadejia Ta Sanar da Ranar Hawan Sallar Gani

0 400

Masarautar nan garin hadejia ta sanar da ranar hawan gani, a wata sanarwa daga Masarautar Hadejia mai dauke da sa hannun Magatakardan Masarauta, Alhaji Abubakar Suleiman; cewa za a gudanar da Bikin Sallar Gani (Sallar Maulidi) ta bana a Hadejia daga ranar Juma’a 5 ga watan Satumba zuwa ranar Lahadi 7 ga Satumba, 2025.

• Hawan farko, zai kasance a ranar Juma’a 5 ga Satumba, 2025 da yamma karfe 3:45.

• Hawan Bariki, Asabar 6 ga Satumba, 2025, karfe 7:00 na safe.

• Hawan Ziyara, Lahadi 7 ga Satumba, 2025, karfe  3:45 na yamma.

Sanarwar tana kara kira ga hakimai da sauran jama’a kan su iso a kan lokaci domin gudanar da zagayen hawa yadda ya kamata.

Leave a Reply