Gwamna Malam Umar Namadi, Ya Rattaba Hannu Kan Dokoki Guda Biyu da Zasu Sauya Tsarin Noma

0 371

Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya rattaba hannu kan dokoki guda biyu da za su sauya tsarin noma daga karamin gwaji zuwa noma na masana’antu a jihar.

A cewar mai magana da yawun sa, Hamisu Mohammed Gumel, waɗannan dokokin za su ƙarfafa kirkire-kirkire, ƙara yawan amfanin gona da kuma haɓaka tattalin arziki ta hanyar noman zamani da kiwon dabbobi.

Dokar farko ta kafa ma’aikatar kiwon dabbobi wadda za ta yi amfani da manyan damar da jihar ke da su a wannan fanni, yayin da dokar ta biyu, wato JATS Law 2025, ta ƙirƙiri hukumar da za ta jagoranci tsarin sauya noma zuwa masana’antu.

Yayin bikin rattaba hannun, Gwamna Namadi ya bayyana cewa Jigawa na ɗauke da ɗaya daga cikin manyan kasuwannin kiwon dabbobi a nahiyar Afrika, inda ya bayyana ma’aikatar a matsayin ginshiƙi na manufofin gwamnatinsa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.