Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Ayyana Yau Laraba A Matsayin Hutun Aiki Domin Bikin Cika Shekaru 34 da ƙirƙirar

0 757

talatin da huɗu da ƙirƙirar jihar

Gwamnatin jihar Jigawa ta ayyana yau Laraba a matsayin hutun aiki domin bikin cika shekaru talatin da huɗu da ƙirƙirar jihar.

An samar da Jigawa ne a ranar 27 ga watan Agustan shekarar 1991 bayan an raba ta daga tsohuwar jihar Kano, a wani shiri na ƙasar baki ɗaya da ya haifar da sabbin jihohi irin su Yobe, Enugu, Bauchi da Kogi domin inganta tafiyar da mulki da haɓaka ci gaba.

A cikin wata sanarwa da shugaban ma’aikatan jihar, Muhammad Dagaceri, ya sanya wa hannu, gwamnati ta ja hankalin jama’a da sukas halarci bukukuwa da addu’o’in hadin kai da aka shirya a sassan jihar don tunawa da wannan rana ta musamman.

Gwamnatin ta ce hutun ba wai kawai don murna ba ne, har ma don ba wa jama’a dama su yi tunani kan ci gaban da jihar ta samu tare dayin addu’a domin samun zaman lafiya da bunƙasar gaba.

Ta kara da cewa wannan bikin na nuna muhimmancin tarihin jihar da kuma ƙarfafa ɗorewar haɗin kai da kishin al’umma a tsakanin mutanen Jigawa.

Leave a Reply