Majalisar karamar hukumar Birniwa ta gudanar da bikin kaddamar da aikin dashen bishiyoyi a fadin yankin karamar hukumar.
Shugaban karamar hukumar, Alhaji Shehu Baba, ya sanar da haka ne yayin da yake kaddamar da aikin. Ya bayyana cewa an Gudanar da bikin dashen ne domin a dasa bishiyoyi a ko’ina cikin karamar hukumar.
Alhaji Shehu Baba , ya kara da cewa wannan aiki yana cikin yunƙurin cimma manufofin gwamnatin jahar karkashin jagorancin Gwamna Umar Namadi ta hanyar dasa bishiyoyi a wurare daban-daban, inda ya lura cewa karamar hukumar na da Yana yanayi daban daban .
Shugaban ya bukaci al’ummar karamar hukumar da su yi gagarumar gudunmawa wajen dasa bishiyoyi da yawa a wannan kakar domin yaƙi da hamada , zaizayar ƙasa, da iska mai ƙarfi.
A cikin jawabinsa, shugaban sashen ayyukan gona da albarkatun ƙasa, Malam Muhammad Aminu Kaugama, ya bayyana cewa karamar hukumar ta karbi itatuwan bishiyoyi 62,000 (dubu sittin da biyu) domin dasawa . Mai Bawa Gwamna Shawara akan harkokin muhalli, Garba Ibrahim , ya gabatar da jawabi kan illolin canjin yanayi, waɗanda suka haɗa da ƙwararowar hamada, zaizayar ƙasa, da mutuwar bishiyoyi masu tarihi. Ya bukaci al’ummar yankin da su dasa bishiyoyi a gidajensu da gonakinsu, tare da gujewa sare bishiyoyi domin kare muhalli daga fadawa mummunan yanayi.