Gwamna Namadi ya bayyana godiyarsa ga al’ummar Dutse bisa tarbar da suka yi masa da tawagarsa

0 188

Gwamna Umar Namadi ya bayyana godiyarsa ga al’ummar karamar hukumar Dutse bisa tarbar da suka yi masa da tawagarsa a lokacin taron gwamnati da jama-a da aka gudanar a yankin.

Gwamna Umar Namadi ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da aniyar kammala aikin samar da ruwa na Great Dutse da aikin gina layin dogo da sauran ayyukan gina hanyoyin gwamnatin tarayya da ke gudana a jihar nan.

Ya ce akwai karin ayyukan gwamnatin jiha da ta tarayya da ke tafe, don haka akwai bukatar jama’a su ci gaba da bayar da goyon baya domin gwamnati ta cimma burinta.

Gwamnan ya yaba wa shugaban karamar hukumar Dutse, Malam Sibu Abdullahi, bisa nasarorin da ya samu. Haka kuma ya gode wa jiga-jigan jam’iyyar APC na yankin bisa hadin kai da kuma kokarinsu na ci gaban magoya bayan jam’iyyar a yankin.

Leave a Reply