Kungiyar Yan Jarida ta kasa reshen Jihar Jigawa zata gudanar da bikin rantsar da sabbin shugabannin ta
Kungiyar Yan Jarida ta kasa reshen Jihar Jigawa, NUJ zata gudanar da bikin rantsar da sabbin shugabanni da kuma wakilan kwamitocin dokoki da Ladabtarwa da Ilimi da kuma na Horaswa na kungiyar.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da sakatariyar kungiyar ta jiha Aisha Ahmed ta rabawa manema labarai.
Ta ce za a rantsar da sabbin shugabanni da wakilan kwamitocin ne a ranar Talata 20 ga watan Mayu 2025 da misalin Karfe goma sha daya na safe a cibiyar yan jaridu ta jiha.
Sanarwar ta kara da cewar shugaban kungiyar NUJ na Jihar Jigawa , Kwamared Isma’ila Ibrahim Dutse, ne zai jagoranci bikin.
Saboda haka, kungiyar ta gayyaci yan jarida da su halarci wannan biki saboda muhimmancinsa.