Gwamna Namadi ya tunatar da yan jam’iyyar APC da su hada kai don tabbatar da nasara a zaben cike gurbi na mazabar Garki da Babura
Gwamna Umar Namadi ya tunatar da magoya bayan jam’iyyar APC a jihar nan da su hada kai don tabbatar da nasara a zaben cike gurbi na mazabar tarayya ta Garki da Babura
Gwamna Umar Namadi ya yi wannan kira ne yayin da yake mika takardar tsayawa takara ga Alhaji Rabi’u Muhktar Garki wanda ya zama dan takarar APC a zaben cike gurbi.
Malam Umar Namadi ya bayyana jin dadinsa da yadda aka gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar da kuma yadda aka fitar da Alhaji Rabi’u Muhktar Garki a matsayin dan takara.
Ya kuma gode wa sauran ‘yan takara bisa nuna hazaka, hadin kai da kishin ci gaban jam’iyyar.
A nasa jawabin, dan takarar APC a zaben cike gurbi na mazabar tarayya ta Garki da Babura, Alhaji Rabi’u Muhktar Garki, ya nuna godiya ga Allah Madaukakin Sarki bisa zabarsa a matsayin dan takarar APC, sannan ya nemi goyon bayan kowa da kowa don samun nasara a zaben.
Ya kuma mika irin wannan godiya ga Gwamna Umar Namadi da shugabannin APC na jihar da mutanen Babura da kuma Garki.