Shekara guda kenan tun bayan hakuncin Kotun Koli dangane da cin gashinkan kananan hakumomi shin ko ina aka kwana
An shiga takun saka dangane da gaza aiwatar da hukuncin kotun koli da ya bai wa kananan hukumomi cikakken yancin cin gashin kansu, amma shekara guda babu labari, abin da ya sanya kungiyoyin ma’aikata kananan hukumomi nuna yar yatsa a kan lamarin.
Shekara guda ke nan cur da kotun kolin ta yanke wannan hukunci da ya haifar da ɗoki a tsakanin ma’aikatan kananan hukumomi 774, sai dai kuma shiru kake ji kamar an shuka dusa,.
Har yanzu babu wata karamar hukuma da aka fara bai wa kudin nata kai tsaye, har yanzu gwamnoni ke karba kudadden. Kuma wannan ya harzuka wasu kungiyoyin farar hula da suka fara nuna ‘yar yatsa kan cewa an fa kure hakurinsu.
Ta dai kai ga kungiyar kananan hukumomi sake daukar matakin shari’a a kan wannan lamari na bai wa kananan hukumomi ‘yancin cin gashin kansu ta hanyar ba su kudadensu kai tsaye daga mataki na kasa
Tun farko dai an fara da samun cikas a kan aiwatar da hukuncin inda aka fara da ɗaga kafa na watanni uku ga gwamnoni, sannan gwamnatin tarayya ta kafa kwamiti mai mutane 10 domin duba aiwatar da hukunci.