Gwamna Ortom Ya Janye Karar Da Ya Shigar Kan Dr Titus Zam da INEC

0 195

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwe ya janye karar da ya shigar kan Dr Titus Zam na jam’iyyar APC da kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC a kotun sauraron kararrakin zabe ta Sanata.

Titus Zam ya samu kuri’u dubu 143 da 151 kuma ya doke Samuel Ortom wanda ya samu kuri’u dubu 106 da 882 inda ya lashe kujerar Sanatan Benue ta Arewa maso Yamma a zaben ‘yan majalisar kasa da aka gudanar ranar 25 ga watan Fabrairu.

Samuel Ortom ya bayyana hakan ne a jiya bayan ganawa da ‘yan majalisar zartarwa na jihar, da ‘yan jam’iyyar PDP, da masu ruwa da tsaki a shiyyar B da majalisar yakin neman zaben sa ta Sanata a Makurdi, babban birnin jihar.

Ya ce ya yanke shawarar janye karar ne saboda dalilai na zaman lafiya duk da rashin gaskiya a zaben. Ya yi alkawarin cewa a matsayinsa na shugaban jam’iyyar PDP, zai goyi bayan jam’iyyar tare da hadin gwiwar sauran shugabanni domin samun damar magance kura-kurai da koma bayan da take fuskanta a halin yanzu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: