Gwamna Uba Sani Ya Bayyana Cewa Talauci da Rashin Aikin Yi Ne Tushen Matsalar Tsaro A Arewa

0 373

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya bayyana cewa talauci, rashin aikin yi, karancin makarantu, asibitoci da harkokin kasuwanci a yankunan karkara a matsayin tushen aikata laifuka, inda ya jaddada cewa shugabanni dole ne su ɗauki alhakin magance matsalar.

Gwamnan ya yi wannan gargadi ne a wajen kaddamar da littafin “Where I Stand” na marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, wanda Sheikh Ibrahim Jalo Jalingo ya fassara zuwa harshen Larabci.

Ya kuma shawarci jam’iyyun adawa da su daina siyasantar da batun tsaro da ikirarin cewa za a iya murkushe ‘yan bindiga ta hanyar yi musu ruwan bama-bamai.

Gwamna Sani, wanda ya wakilci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a wajen taron a matsayin Babban Bako na Musamman, kuma shi ne Mai masaukin baki, ya bayyana cewa rashin tsaro a yankin Arewa maso Yamma ya bambanta da ta’addancin Boko Haram na Arewa maso Gabas da ke da ra’ayin addini. Ya ce a nan talauci, rashin aikin yi da sakaci da yankunan karkara su ne tushen matsalar ‘yan bindiga.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa yawan ma’aikatan tsaro a Najeriya ya ragu duk da ƙaruwa mai yawa da aka samu a yawan jama’a cikin shekaru 45 da suka wuce.

Leave a Reply