UNICEF da Biritaniya Sun Tallafa Wa Jigawa da Gine-Gine Masu Jure Sauyin Yanayi

0 508

Wasu rahotanni da sawaba radiyo ta samu sun bayyana cewa gwamnatin Biritaniya da UNICEF sun miƙa wasu sabbin kayayyaki da ayyukan gine-gine masu jure sauyin yanayi ga gwamnatin Jihar Jigawa, musamman ga makarantu da asibitocin ƙananan yara.

Wakiliyar UNICEF a Najeriya, Wafaa Saeed, ta ce Najeriya tana cikin ƙasashen da ke fuskantar haɗarin bala’in yanayi kamar ambaliya, fari, da tsananin zafi, wanda ke cutar da miliyoyin yara a kowace shekara.

Aikin CRIBS, wanda aka aiwatar tare da haɗin gwiwar jihohin Kano da Jigawa, ya mayar da hankali kan samar da ingantattun gine-gine na kiwon lafiya da ilimi da za su iya jure bala’o’in yanayi.

Gwamnan Jigawa, Umar Namadi, ya bayyana godiya ga hukumomin, inda ya ce wannan aikin zai taimaka wajen rage illolin ambaliya da sauran matsalolin da ke addabar jihar kowace shekara.

Leave a Reply