Rugujewar Gini A Jigawa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutum ɗaya da Jikkatar Wasu Bakwai

0 702

Mutum ɗaya ya rasu yayin da wasu bakwai suka jikkata a rugujewar wani gini da ruwan sama ya haddasa a ƙauyen Kabak, karamar hukumar Kirikasamma, jihar Jigawa.

Jami’in yaɗa labarai na karamar hukumar, Musa Muhammad, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce mutum biyar aka kwantar a asibiti yayin da aka sallami biyu bayan samun magani.

Shugaban karamar hukumar, Muhammad Maji, ya ziyarci wurin tare da bayar da tallafin kuɗi domin kula da wadanda suka jikkata da kuma iyalan da suka rasa ɗan uwansu.

Lamarin ya zo ne a daidai lokacin da ake cigaba da fuskantar matsalar rushewar gine-gine a sassa daban-daban na ƙasar, musamman a biranen Abuja da Lagos.

Leave a Reply