Gwamnan Jigawa Umar Namadi ya yaba da shekaru biyu na shugabancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu

0 164

A wata hira ta musamman da jaridar LEADERSHIP, Gwamnan Jihar Jigawa Malam Umar Namadi ya yaba da shekaru biyu na shugabancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana kiran su da matakai masu ƙarfi da sauye-sauyen da suka dace da ci gaban ƙasa.

Ya bayyana cewa cire tallafin mai da daidaita darajar canjin kuɗi sun kasance matakai masu wahala amma wadanda ake buƙata, waɗanda suka ƙara yawan kuɗaɗen shiga ga gwamnati da taimakawa daidaita tattalin arzikin ƙasa.

Gwamna Namadi ya ce waɗannan kudirori ne da suka ba Jigawa damar gudanar da ayyuka da dama, ciki har da gina tituna, da gyaran cibiyoyin lafiya, da bunƙasa fannin noma da na ilimi. Ya tabbatar wa al’umma cewa fa’idar waɗannan sauye-sauyen tuni ta fara bayyana, kuma sauran alheri na tafe.

Leave a Reply