Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya sanar da dakatar da wutar lantarki a jihohin Arewa maso Gabas saboda aikin gyara babban layin wutar lantarki na 330kV a Bauchi.
Aikin zai gudana ne daga ranar 10 ga watan Yuni zuwa 14 ga watan, inda yankuna kamar Damaturu, da Yola, da Jalingo da Molai za su fuskanci daukewar wutar gaba daya, yayin da Gombe da Biu za su dogara da tashar samar da wutar ta Dadin Kowa.
Kamfanonin rarraba lantarki na Yola da Jos sun tabbatar da matsalar, inda suka bayyana cewa ƙarancin isar da wuta daga TCN da gyare-gyaren da ake yi a Bauchi ne suka haddasa matsalar wutar a tsakanin al’umma. Wannan matsala na zuwa ne bayan watanni takwas da wata irin matsalar ta jefa jihohi 17 na Arewa cikin duhu, lamarin da ya sake bayyana rashin daidaitaccen tsarin rarraba wutar lantarki a Najeriya.