Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya ƙara albashin ma’aikatan manyan makarantu na gwamnati da kashi 70%
Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya ƙara albashin ma’aikatan manyan makarantu na gwamnati da kashi 70% bisa sabon tsarin CONPCASS/CONTEDISS 2024, wanda zai fara aiki daga Oktoba 2025. Wannan mataki na cikin shirin gwamnatin jihar na inganta walwalar ma’aikata da farfaɗo da harkar ilimi.
A yayin wani zama da aka yi tsakanin gwamnan da shugabannin ƙungiyoyin ma’aikata (JUTIKS), an cimma matsaya wacce ta kai ga janye yajin aikin wata guda da ma’aikatan suka shafe suna yi.
Ƙungiyoyin ma’aikata sun yaba da jajircewar gwamnan wajen kare haƙƙinsu da bai wa ilimi fifiko. Haka kuma, sun jinjina wa gwamnati bisa rabin kuɗin makaranta (50%) da ta rage, da kuma gyare-gyaren gine-gine da kayan aiki a cibiyoyin ilimi.