Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da murabus ɗin Geoffrey Uche Nnaji, Ministan Kirkire-Kirkire, Kimiyya da Fasaha, bayan zarge-zargen da aka yi masa kan amfani da da takardun bogi.
Nnaji, wanda aka nada a watan Agusta 2023, ya mika takardar murabus dinsa yau, inda ya gode wa Shugaban Ƙasa saboda damar da ya ba shi na yin aiki wa ƙasar.
A cikin wasikarsa, Nnaji ya bayyana cewa ya yanke shawarar sauka daga mukaminsa saboda zarge-zarge da ake yi masa, ya kuma kira hakan da kazafi ne kawai irin na siyasa.
Shugaba Tinubu ya gode masa saboda hidimar da ya bayar, tare da fatan alheri a ayyukan da zai yi nan gaba in Bayo Onanuga, mataimaki na musamman kan yada labarai ga Shugaban kasa.