Alhaji Musa Muhammad yake cewa, yayin da shugabannin ƙananan hukumomi na Jihar Jigawa suka cika shekara ɗaya a ofis, wasu sun sami nasarar gudanar da ayyuka masu gani a fili, yayin da wasu kuma suka gaza nuna abin a zahiri.
A matsayina na ɗan ƙasa mai sha’awar ci gaban yankina, na shaida irin gagarumin ci gaban da wasu tsofaffin shugabanni suka gudanar wanda har yanzu ana iya gani da ido.
Sai dai kuma salon mulkin Abba Ari ya bambanta da manufa ta “12-Point Agenda” na Gwamna Umar Namadi Danmodi.
A cikin shekara ɗaya da ya yi a ofis, babu wani muhimmanci a aikace da za a iya nuna, sai dai hotuna da rubuce-rubuce a kafafen sada zumunta waɗanda yawanci ba sa ƙunshe da gaskiyar abinda ke faruwa.
Aikin da kaɗai ya iya gani shi ne na “Danmodi Talented School”, wanda sunan kawai aka yi amfani da shi wajen yaudarar jama’a, domin ba ya cikin manufar 12-Point Agenda na gwamnatin jihar.
Ina kalubalantar tsarin da aka bi wajen zaɓen ɗaliban makarantar Danmodi Talented School, da kuma rabon keken hawa da aka yi kwanan nan ga ɗalibai — waɗannan abubuwa suna buƙatar karin bayani da gaskiya.
Haka kuma, kwangilar da ake cewa ta kai naira miliyan 60 da aka bayar don fitar da ruwan tafkin abattoir zuwa kogin Hadejia, babban ɓarnar kuɗin jama’a ne.
Wadannan miliyoyin kudade da za a binne a ƙasa, da ya fi dacewa a raba su ga mazabu 11 na yankunan ƙaramar hukumar Hadejia, domin a gudanar da aiyuka na al’umma wanda zai baiwa kowa damar jin daɗin dimokuraɗiyya.
Da ni ne a matsayin Yaro Abba Ari, da na kwaikwayi salon shugabannin baya, domin in bar tarihi mai kyau da za a iya gani da ido.
Alhaji Musa Muhammad
Gabari Quarters, Hadejia, Jigawa.