Gwamnan jihar Katsina ya ce yawan yan bindiga a yankin Arewa Maso Yamma sunfi yawan Jami’an tsaro

0 101

Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya ce yawan yan bindiga a yankin Arewa Maso Yamma sunfi yawan Jami’an tsaro.

Gwamnan ya soki Sojoji da Yan Sanda bisa yadda basa bawa Yan Kato da Gora goyan bayan da suke bukata.

Gwamna Masari ya furta hakan ne a Gidan Gwamnatin Jihar a jiya Talata lokacin da ya karbi bakuncin Ministan Yada Labarai, Alhaji Lai Muhammad.

Gwamna Masari ya bukaci gwamnonin Arewa su dauki yan Bingilanti dubu 3,000 tare da basu makamai.

Dagan an sai Gwamnan ya ankarar da jami’an tsaro kan su dauki matakin gaggawa a kan lamarin.

A kwanan nan ne dai hukumar NCC ta umarci kamfanonin sadarwa da su datse dukkan hanyoyin sadarwar a Jihar Zamfara da kuma wasu Kananan Hukumomi guda 13 na Jihar Katsina a matsayin irin matakan da ake dauka don magance matsalar ayyukan ’yan bindiga a yankin.

Kazalika, sojoji kuma na ci gaba da luguden wuta ta sama da ta kasa ga ’yan bindigar da suka kafa sansanoni a dazukan yankunan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: