Gwamnan Nasarawa Abdullahi Sule ya fada sana’ar da zai koma bayan ya kammala wa’adin mulkinsa

0 367

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi magana kan sana’ar da zai koma bayan ya kammala wa’adin mulkinsa. Gwamna Sule ya bayyana shirinsa na komawa sana’ar da ya fara da ita ta asali wato aikin walda, da zarar ya kammala wa’adin mulkinsa a shekarar 2027.

Jaridar The Nation ta ce Gwamna Sule ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wani taron tattaunawa da hukumar samar da wutar lantarki ta karkara (REA) ta shirya tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar Nasarawa.

Ya kuma yi amfani da damar wajen tabbatarwa da masu sha’awar zuba jari cewa jihar Nasarawa na da ƙwararrun ma’aikata, ya nuna cewa jihar na da ɗimbin matasa masu horo da shaidar ƙwarewa da za su iya tallafawa masana’antu.

Leave a Reply