Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya koka kan wata maƙarlashiya da ake shirya gwamnatinsa da kuma karan kansa Hyacinth Alia ya bayyana cewa ya gano shirin wasu masu tayar da hargitsi tare da ɓata sunan gwamnatinsa domin a ayyana dokar ta ɓaci a jihar Gwamnan ya nuna cewa daga cikin abin da masu mugun nufin suke so shi ne su ga an raba shi da kujerarsa ta mulkin jihar Benue.
Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya bayyana wata maƙarƙashiya da ake ƙulla masa. Gwamna Hyacinth Alia ya bayyana cewa akwai wani yunkƙri mai hatsari da ake ƙoƙarin aiwatarwa domin tayar da zaune tsaye a jihar da nufin cire shi daga kan kujerarsa.