Gwamnati ta biya tallafin man fetur kimanin ₦169.4Bn domin farashin lita ya tsaya kan ₦620

0 365

Duk da tabbataci da hawa teburin naki da shugaban kasa Bola Tinubu yayi tare da kafewa kan cewa tallafin man fetur ya tafi, binciken jaridar Dailytrust ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta biya naira biliyan 169.4 a matsayin kudin tallafin man fetur, domin tsayar da farashin man a kan naira 620 kowace lita.

Rahotanni da dama sun bayyana cewa fashin man har yanzu bai tashi ba, duk da tashin farashin sauyin kudi nan dala da kuma karuwar farashin danyen manfetur zuwa dala 95 akan kowace ganga.

Wani takarda da kwamitin raba asusun gwamnatin tarayya, wanda Daily Trust ta gani a jiya, ya nuna cewa a watan Agustan 2023, kamfanin albarkatun man fetur ta Najeriya ta biya Naira miliyan 275 a matsayin rara ga Najeriya ta hannun kamfanin NNPC.

Kamfanin NNPC ya yi amfani da Naira biliyan 169.4 a matsayin naira 770 akan dala daga cikin dala miliyan 275 wajen biyan tallafin man fetur. Sannan NNPC ta rike dala miliyan 55, ba bisa ka’ida ba. Tonon sililin da kwamitin raba asusun gwamnatin tarayya ya yi ya nuna cewa tallafin ya dawo kuma kamfanin na NNPC na karbar ribar NLNG don biyan tallafin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: