Gwamnatin APC ce ke daukar nauyin rikicin da ke faruwa a jam’iyyun LP, PDP da NNPP – El-Rufai

0 95

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce akwai hannun Gwamnati mai ci a rikicin da ke addabar jam’iyyun adawa a kasar nan.

Jaridar The Guardian ta rawaito cewa El-Rufai ya yi wannan ikirari ne yayin da ya ke jawabi ga wasu mambobin jam’iyyar SDP, wacce ya sanar da komawa cikin ta a jiya Litinin.

Tsohon gwamnan ya kuma bayyana cewa akwai mutane da aka dauka aiki domin haddasa rikici a jam’iyyun adawa.

Ya ce, “Rikicin da ke cikin jam’iyyar Labour Party gwamnati mai ci ce ta haddasa shi. Kowa ya sani. Tsallake-tsallake daga kotu zuwa kotu duk wata dabara ce domin shagaltar da shugabancin jam’iyyar daga gudanar da aikinsu yadda ya kamata. Haka nan ake yi wa PDP, har ma NNPP ma an sa ta a gaba domin a rusa ta. Akwai mutanen da aka ba albashi domin su je su haddasa fitina a NNPP.

“Abin karshe da na karanta game da NNPP shi ne cewa wani bangare na jam’iyyar ya kori Kwankwaso da gwamna mai ci. Idan ka ga irin wadannan abubuwa, ka san cewa rikicin da aka kirkira ne.

“Wace jam’iyya ce ke korar gwamna mai ci, kuma shi kadai ne gwamnan da suke da shi? Ka sani cewa rikicin da aka shirya ne. Ba ni da cikakken bayani. Ba zan ambaci komai ba domin ba ni da cikakken bayani.”

– Daily Nigerian

Leave a Reply