Gwamnatin Jigawa ta bada miliyan 14 domin yan takarar da sukayi nasara a musabakar Karatun Alqurani

0 448

Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da kudi fiye da naira miliyan goma sha hudu domin nemowa yan takarar Jigawa da suka yi bajinta a musabakar Karatun Alqurani da aka gudanar a Jihohin Yobe da kuma Kebbi guraben karatu a kasar Morocco

Sakataren zartarwa na hukumar bada tallafin karatu ta jiha Mallam Saidu Magaji ya sanar da hakan a lokacin da yake tilawar nasarorin da hukumar ta samu a wannan shekara

Ya ce daliban su goma sun sami matsayin na daya dana biyu da kuma na uku a musabakar da aka gudanar a jihohin Yobe da kuma Kebbi

Mallam Saidu Magaji ya kara da cewar za a nemowa daliban karatun digiri a bangarori daban daban

Yana mai cewar gwamnatin jiha zata kara tura dalibai guda dari zuwa kasar Cyprus domin yin karatun likita yayinda za a tura malaman makarantun Jigawa su dari domin yin karatun digiri na biyu ko kuma Dokta.

Sakataren ya kuma ce nan bada jimawa zasu fara aikin tantance sabbin dalibai da kuma cigaba da biyan tsaffin dalibai tallafin karatu

Leave a Reply