Mazauna Jigawa sun bayyana rashin amincewarsu da sabon kudin wutar lantarki da Kamfanin KEDCO ya fitar musu
Mazauna jihar Jigawa sun bayyana rashin amincewarsu da sabon kudin wutar lantarki da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO) ya fitar musu, suna cewa ba su da ikon biyan kudin, musamman ganin cewa wutar ba ta da tabbas kuma tana yawan yankewa.
Mutanen da abin ya shafa sun bayyana cewa kudin wuta da aka musu a watan Afrilu ya yi tsanani, duk da cewa basu samu ingantaccen wuta ba tsawon watanni uku zuwa hudu da suka gabata.
A cewar Ali Ahmadu, wani jagoran al’umma daga Takur Quarters a Dutse, Wutar da KEDCO ke kawowa ba ta da tabbas, sau da yawa suna yini ko fiye ba tare da wuta ba.
Wannan ya sa jama’a ke kiran gwamnati da ta sa baki domin magance matsalar, suna mai cewa ba za su iya ci gaba da biyan kudin wuta da ba su amfani da ita yadda ya kamata ba.
A nasa bangaren, wani ɗan gwagwarmaya a jihar, Comrade Shu’aibu Kafingana, ya bayyana cewa lamarin ya tayar da kura a tsakanin mazauna jihar, inda mutane ke kira da a tabbatar da adalci da gaskiya a harkar rabon wuta. Comrade Kafingana ya kuma yi kira ga hukumar kula da harkokin wutar lantarki (NERC) da ta duba rahoton kararraki daga Jihohi kamar Jigawa tare da tilasta bin doka da oda ga kamfanonin rarraba wuta.