Gwamnatin Jihar Jigawa ta hannun Ma’aikatar Kula da Kananan Hukumomi ta sanar da dakatar da wasu kansiloli masu kula da sassa da kumaKansiloli masu Gafaka daga mukamansu nan take.
A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na ma’aikatar, Najib Umar, ya fitar a madadin Kwamishinan Kananan Hukumomi na jihar, an bayyana sunayen jami’an da dakatarwar ta shafa.
Wadanda aka dakatar sun hada da Kansiloli masu Gafaka Bala Energy, da kuma Abdullahi Usman. Sai kuma masu bada shawara ta musamman daga ciki akwai Afake Auyo, Ussaini Biyuta Kataudi, da kuma Kande Auyo.
Sanarwar ta umarci dukkan wadanda abin ya shafa da su gaggauta mika dukkan kayayyakin gwamnati da ke hannunsu ga Daraktan Mulki na Karamar Hukumar Auyo ba tare da wani bata lokaci ba.
Dakatarwar ta biyo wani matakin dakatarwa da aka dauka a baya-bayan nan, tun bayan zaben fidda gwani dan takarar majalissar tarayya mai wakiltar Hadejia, Auyo da Kafin Hausa da kuma zargi yin wasu kalamai da tarurruka na tunzura ‘yan jam’iyya a karamar hukumar Auyo.