Wasu ‘yan bindiga sun kai hari gidajen kwanan dalibai na makarantar Federal Polytechnic Kaura Namoda da ke Kaura Namoda a jihar Zamfara State, inda suka yi garkuwa da dalibai bakwai.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Yazid Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa harin ya auku ne a a cikin dare.
A cewarsa, ‘yan bindigar sun zo ne ta hanyar wucewa, inda suka tarar da daya daga cikin gidajen kwanan daliban a bude. Daga nan ne suka kutsa cikin gidan tare da sace dalibai bakwai zuwa wani wuri da ba a sani ba.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta ce tuni jami’an tsaro suka fara gudanar da bincike da kuma kokarin ceto daliban da aka sace. Haka kuma, an baza jami’an tsaro a yankin domin bin sawun maharan da tabbatar da dawo da zaman lafiya.
Lamarin ya sake jefa al’umma cikin fargaba, musamman a yankunan da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga a jihar Zamfara.