Atiku: Kowa Na Cikin Haɗari Saboda Rashin Tsaro a Najeriya a Mulkin Tinubu

0 219

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa matsalar rashin tsaro a Najeriya ta kai wani mataki mai matuƙar tayar da hankali, inda ya ce babu wanda ke jin cikakken tsaro a ƙasar.

Atiku ya ce hare-haren ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane na ci gaba da barazana ga rayuka da dukiyoyin al’umma, yana mai zargin gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu da gaza kawo ƙarshen matsalar.

A cewarsa, rashin tsaron ya kai matsayin da babu mai kuɗi, talaka, tsoho ko yaro da zai iya cewa yana da tabbacin kare rayuwarsa ko dukiyarsa idan ya fita daga gida.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa yanayin da ake ciki ya nuna buƙatar ɗaukar matakan gaggawa domin dawo da zaman lafiya da kare rayukan al’umma.

Atiku ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ƙara bai wa jami’an tsaro kayan aiki na zamani, horo da cikakken goyon bayan da suke buƙata domin yaƙi da ‘yan ta’adda, masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka a faɗin ƙasar.

Ya jaddada cewa inganta tsaro shi ne ginshiƙin ci gaba, tare da kira ga gwamnati da ta ɗauki matakai masu tasiri domin magance matsalar da ta addabi al’ummar Najeriya.

Leave a Reply