Gwamnatin Jihar Jigawa tana gudanar da aikin shimfida bututun samar da ruwan sha mai tsawon kilomita 28 kan kudi naira miliyan 529 a garin Kazaure.
Manajan Daraktan hukumar samar da ruwan sha ta jiha Injiniya Zaiyan Rabiu ya sanar da hakan a lokacin da ya kai ziyarar gani da ido wuraren aikin.
- Kotu ta ɗage shari’ar Nnamdi Kanu har sai baba ta gani
- Yan bindiga sun kai hari wani masallaci a garin Sabon Birni
- Kwamitin zakka na masarautar Hadejia ya kaddamar da rabon zakkar da aka tattara a kauyen Masassadi
- Ma’aikatan lantarki na Kaduna sun dakatar da yajin aiki
- NAFDAC ta buƙaci a riƙa yanke wa masu jabun magunguna hukuncin kisa
Yace aikin idan an kammala zai maraba ya ga ayyukan gwamnatin tarayya na inganta samar da ruwan sha a garin Kazaure ta hanyar tura ruwan zuwa cikin garin Kazaure.

Injiniya Zaiyan Rabiu ya kara da cewa idan an kammala aikin zai samar da lita miliyan uku ta ruwa ga garin Kazaure a kowacce rana.
Daga nan ya jaddada kudirin gwamnatin jiha na cigaba da samar da ruwan sha mai tsafta a kowane lungu da sako na jiharnan.