Gwamnatin jihar Borno ta ware naira biliyan 8.7 domin inganta  tsaftar muhalli kamar yadda asusun yara na majalisar dinkin duniya UNICEF ya yi alkawari, domin tabbatar da ganin an samu karuwar jama’a da tsaftar ruwan sha a jihar.

Babban Manaja na Hukumar Samar da Ruwa da Tsaftar Ruwa ta Jihar Borno (RUWASSA), Dakta Musa Ali, ya ce gwamnati ta bayar ta amince da sake gina wasu madatsun ruwa guda shida domin magance kalubalen da rikicin Boko Haram ya haifar shekaru 13 da suka gabata.

Ya kuma bukaci abokan hadin gwiwa da kungiyoyi masu zaman kansu na kasa da kasa, akan suke wayar da kan jama’a akan su daina bahaya a bainar jama’a domin ceton rayuka.

Manajar hukumar UNICEF a Maiduguri, Mamita Bora Thakkar, ta ce kungiyar za ta tallafawa gwamnati don tabbatar da cewa dukkanin kananan hukumomin jihar ba’ayin bahaya a bainar jama’a.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: