Gwamnatin jihar Filato za ta samar da na’urori na zamani domin magance matsalar tsaro

0 199

Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya ce gwamnatin jihar za ta samar da fasahar zamani da sauran na’urori na zamani domin magance matsalar rashin tsaro a jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a jiya Juma’a a Jos.

Gwamnan yace rashin tsaro ya kasance babban kalubalen da gwamnatinsa ta fuskanta a cikin shekara guda, gwamnan ya godewa gwamnatin tarayya bisa goyon bayan ta ga kokarin gwamnatin jihar wajen shawo kan lamarin.

Ya yi bayanin cewa gwamnatinsa ta horas da jami’an tsaro sama da 600 na rundunar tsaro ta jihar, da aka yiwa take da Operation Rainbow, don tallafa wa jami’an tsaro a fannin tattara bayanan sirri.

Mutfwang ya yi alkawarin bayar da goyon baya ga hukumomin tsaro a kokarinsu na magance matsalar rashin tsaro a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: