Gwamnatin Jihar Jigawa tace tana kokari wajen gyaran hanyoyi da ruwan sama ya lalata

0 66

Gwamnatin jihar Jigawa tace tana bakin kokarinta wajen gyaran hanyoyi da kwalbatoci da ruwan sama ya karya domin baiwa masu ababan hawa da sauran al’umma damar tafiye-tafiye.

Babban sakataren ma’aikatar ayyuka da sufuri ta jiha, Injiniya Datti Ahmed ya sanar da hakan ta cikin shirin Radio Jigawa.

Yace a yanzu haka gwamnati ta kai kayayyakin aiki domin gyaran hanyar Baranda da ruwa ya yanka, amma yawaitar ruwan saman da ake samu yana jawo tafiyar hawainiyar da aikin ke yi.

Injiniya Datti Ahmed ya kara da cewar gwamnati ta gyara wuraren da ruwa ya yi ta’adi akan hanyar Jahun zuwa Gujungu, yayin da zuwan ruwa ya hana aikin gyaran da ake yi akan hanyar Kiyawa zuwa Jahun.

Dangane da hanyoyin gwamnatin tarayya da ruwan ya yiwa taadi a jihar nan kuwa, babban sakataren yace tuni suka sanar da kwantirolan aiyuka na tarayya a jihohin Jiagawa da Bauchi akan lalacewar gadar Tsamiyar Tarnada da Gadar Masaya da titin Karnaya da na Kiyawa da kuma kan titin Fatara.

Ya kara da cewa jami’ai daga gwamnatin tarayya sun ziyarci wuraren domin gani da ido, inda kuma ya bukaci masu ababan hawa dasu guji tafiyar dare saboda hadarin dake tattare da hakan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: