Majalissar masarautar Gumel ta bayyana ranakun gudanar da sallar Gani ta bana.

0 72

Majalissar masarautar Gumel a jihar Jigawa ta bayyana ranakun gudanar da sallar Gani ta bana.

Sakataren majalissar kuma Majidadin Gumel, Alhaji Murtala Aliyu ya tabbatar da hakan ga manema labarai.

Yace za a gudanar da bukukuwan sallar Ganin ne a ranakun Juma’a, Asabar da kuma Lahadi,wanda ya kama daga 7, 8 da kuma 9 ga watan gobe na Oktoba idan Allah ya kaimu.

Murtala Aliyu ya kara da cewar tuni aka sanar da hakimai da Dagatai da masu unguwanni domin yin shirin gudanar da bikin na Gani na bana.

A wani labarin kuma, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kirikasamma, Birniwa da Guri, Dr Abubakar Hassan Fulata ya raba kayan abinci da sauran kayayyaki na kudi naira dubu 600 ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Musari da Takazza a karamar hukumar Guri.

Da yake jawabi a wajen bikin, Dr Abubakar Hassan Fulata ya ce ya yi hakan ne domin rage musu radadin da suke ciki.

Kayayyakin da aka bayar sun hada da buhunan garin kwaki guda 10 da buhunan sikari 4 da fatun buhuna guda 100 domin aikin jinga.

Leave a Reply

%d bloggers like this: