An sake ganowa wasu gawarwakin mutane biyar a wani hatsarin kwale-kwale a karamar hukumar Ringim da ke jihar Jigawa

0 105

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta ce ta sake gano wasu gawarwakin mutane biyar a wani hatsarin kwale-kwale a karamar hukumar Ringim da ke jihar.

A baya Sawaba ya ba da rahoton yadda mutane biyu suka mutu sannan wasu shida suka bace a hadarin kwale-kwalen da ya afku a ranar Lahadi.

A wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan ta fitar ta ce daga cikin mutane shida da suka bata, an sake gano gawarwakin mutane biyar.

Da wannan lamari, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Lawan Shiisu Adam, ya ce adadin wadanda suka mutu sakamakon hadarin kwale-kwalen ya karu zuwa bakwai.

Shiisu Adam ya ce wadanda lamarin ya rutsa da su a ranar Lahadi mazauna garin Dabi ne da ke balaguron jaje zuwa kauyen Siyangu.

Rundunar ‘yan sandan ta ce akwai mutane 13 a cikin kwale-kwalen da ya kife, inda aka ceto wasu biyar.

Lamarin ya faru ne bayan faruwar irin haka sau uku a kananan hukumomin Miga, Gwaram da Guri na jihar wadanda suka jawo mutuwar mutane 12 galibi mata da yara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: