Gwamnatin jihar Jigawa zata hada gwiwa da wata kungiyar Kwararrun Likitoci domin kula da bukatun lafiyar masu karamin karfi

0 59

Gwamnatin jihar Jigawa zata hada gwiwa da wata kungiyar Kwararrun Likitoci mai suna Physicians across the continent wajen kula da bukatun lafiyar masu karamin karfi a cikin al’umma a jihar nan.

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya bayyana haka lokacin da ya karbi bakuncin babban jami’in kungiyar a kasar nan Dr Shamsidden Fagbo wanda ya kai masa ziyarar ban girma a gidan gwamnati.

A cewarsa, Gwamnatinsa na maraba da ayyukan kungiyar domin zasu tallafawa kudirinta na inganta lafiyar al’umma musamman masu fama da larura iri daban daban da ba su da halin zuwa asibiti don kula da lafiyarsu.

Alhaji Muhammad Badaru Abubakar daga nan ya umarci babban sakataren ma’aikatar lafiya ya tattauna da Kungiyar kan fannonin da zasu bada gudummawa da kuma tallafin da gwamnati zata basu wajen samun nasarar gudanar da ayyukansu.

Tun farko a nasa jawabin babban Daraktan kungiyar Dr Shamsudden Fagbo ya ce sun zo jihar nan domin yin hadin gwiwa da gwamnatin jiha wajen gudanar da ayyukan lafiya ga masu karamin karfi.

Ya ce kungiyar wanda take zaune a kasar Birtaniyya na samun tallafi daga kasar Saudiyya, inda yanzu haka ta gudanar da ayyuka a kasashe 41 kuma kimanin mutane dubu dari uku ne suka amfana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: