Hukumar kula da kogin Hadejia-Jama’are ta fara gudanar da gangamin yashe kogin

0 87

Hukumar kula da kogin Hadejia-Jama’are ta fara gudanar da gangamin yashe kogin domin bikin tunawa da ranar kare Koguna ta Duniya.

An kaddamar da gangamin ne a Kogin Challawa dake karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano a shirye-shiryen gudanar da bikin na bana.

Manajan Daraktan hukumar, Alhaji Ma’amun Da’u Aliyu ya bayyana cewa ana gudanar da bikin ne domin yin karin haske kan amfanin kuguna tare da kara sanar da al’umma muhimmancinsu.

Ya ce an shirya gudanar da gangamin yashe kogin ne domin fadakar da al’umma illolin dake tattare da gurbatar ruwa.

Manajan Daraktan ya kara da cewa tasirin wasu ayyukan al’umma da na yanayi ne ke haifar da matsalar karancin ruwan sha a biyo bayan sauyin yanayi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: