Rundunar Yan Sandan jihar Kano ta kama wani mutum bisa zarginsa da yunkurin yin garkuwa da mutum

0 96

Rundunar Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum bisa zarginsa da yunkurin yin Garkuwa da mutum a kyauyen Soro Daya, na karamar hukumar Tsanyawa ta Jihar.

Kakakin rundunar Yan Sanda ta Jihar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce wani mutum ne ya kai musu korafin cewa, wani ya kira shi ta waya tare da yi masa barazanar sace Dansa ko kuma ya biya Naira Miliyan 1.

DSP Haruna Kiyawa, ya ce bayan karbar rahotan ne, Kwamishinan Yan sandan Jihar Malam Sama’ila Dikko, ya umarci rundunar yaki da Garkuwa da mutane karkashin SP Shehu Dahiru su kamo mai yin masa bazanar domin gurfanar dashi a gaban Kotu.

Haka kuma ya ce bayan zurfafa bincike, sun gano mutumin dan uwansa ne kuma wanda ake zargin ya amsa laifinsa na cewa ya yi masa barazana ta wayar tarho.

Kazalika, ya ce za’a gurfanar da mutumin a gaban Kotu bayan kammala bincike.

Leave a Reply

%d bloggers like this: