Kimanin Jami’an tsaron Sudan 5 aka kashe, a lokacin da suke wani bincike a birnin Khartoum.

Hukumomin sun dora Alhakin kaiwa harin kan Kungiyar masu ikirarin Jahadi na Isis.

Hukumomin tsaro na Fasaha a kasar sun ce kimanin mutane 11 suka kama a kasar, kuma dukkanin su yan kasashen waje ne.

Kawo yanzu shafukan kafafen yada labaran kasar basu dora alhakin kaiwa harin kan Kungiyar Isis ba.

Kazalika, Kungiyar ISIS bata bayyana cewa ita ce ta dauki nauyin kaiwa harin ba.

Amma Kasar Amurka, ta bayyana cewa akwai yiwuwar ISIS su shiga kasar ta Sudan.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: