Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya mika sakon ta’aziyarsa ga Shugaban Jam’iyar PDP

0 93

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar, ya mika sakon ta’aziyarsa ga Shugaban Jam’iyar PDP na Jihar Jigawa Alhaji Babandi Ibrahim Gumel, biyo bayan mutuwar matarsa.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da Babban Mataimaka masa kan Sabbin Kafafen Yada Labarai Auwal Danladi Sankara, ya rabawa manema labarai a Dutse.

A cewarsa, Gwamna Badaru Abubakar ya bayyana mutuwar matar Shugaban Jam’iyar a matsayin babban rashi ga Jihar nan, inda ya yi addu’ar Allah ya jikanta da rahama da kuma bawa Iyalanta hakurin jure rashin.

Idan za’a iya tunawa de a ranar Litinin din nan ne, Allah ya karbi rayuwar Hajiya Talatu Babandi Ibrahim, tana da shekaru 49 a Duniya.

Kuma ta rasu ne a Babban Asibitin Kwanciya na Gumel, bayan gajeriyar rashin lafiya.

Marigayiyar ta rasu ta bar Mijinta Hon Babandi Ibrahim Gumel, da yaya 4 da kuma yan Uwa.

Kuma tuni aka binne ta kamar yadda Addinin Musulunci ya tanadar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: