Mutane 34 aka kashe jiya a jihar Kaduna

0 45

Akalla mutane 34 aka kashe jiya lokacin da wasu mutane dauke da makamai suka kai hari a garin Madamai dake karamar hukumar Kaura ta jihar Kaduna. Wasu mazauna garin da dama kuma sun jikkata a harin.

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, wanda ya tabbatar da harin, ya yi Allah wadai da shi tare da yin kira ga hukumomin tsaro da su zakulo wadanda suka kai harin.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce gwamnatin jihar za ta dauki nauyin maganin wadanda suka jikkata.

Ya ce saboda haka Gwamna El-Rufai ya umarci Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna da ta tantance lamarin da nufin taimakawa iyalan wadanda abin ya shafa.

Ya jajantawa iyalan wadanda abin ya rutsa da su tare da yin addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu.

El-Rufa’i ya yi kira da a kwantar da hankula sannan ya bukaci hukumomin tsaro da su kara kaimi wajen farautar masu laifin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: