Hare-haren jiragen saman yaki na sojojin Najeriya sun kashe masunta akalla 20 bisa kuskure a wani sansanin mayaka dake jihar Borno.

Majiyoyi sun ce jirgin yakin saman Najeriya a ranar Lahadi yayi luguden wuta a Kwatar Daban Masara dake tafkin Chadi, wanda yayi iyaka da kasashe makota na Nijar da Chadi da Kamaru.

Yankin shine babban sansanin mayakan ISWAP.

Rahoton adadin wadanda aka kashe yazo kasa da mako biyu bayan jami’ai sun sanar da cewa wani harin sama kan wani kauye ya kashe fararen hula 9 a arewa maso gabas.

A ‘yan kwanakinan kungiyar ISWAP ta janye haramcin hana kamun kifi a wajen, inda ta bawa masunta dama su shiga ruwa su kama kifi a kyauta. Hakan ya jawo karuwar masunta wadanda a baya suka tsere daga yankin.

Labarin aukuwar lamarin yazo ne sannu a hankali saboda karancin layin sadarwa a yankin.

Wani mai magana da yawun dakarun sojin saman Najeriya, bai amsa sakon wayarsa ba domin samun tabbacin labarin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: