Gwamnatin jihar Jigawa zata yi hadin guiwa da Kamfanin Galaxy Backbone

0 258

Gwamnatin jihar Jigawa zayi hadin guiwa da Kamfanin Galaxy Backbone, GBB, domin bunkasa hada-hadar fasahar zamani da ci gaban ababen more rayuwa a Najeriya.

Sawaba Radio ta gano haka ne a lokacin da Gwamna Malam Umar Namadi ya kai ziyarar aiki a hedikwatar Galaxy Backbone da ke Abuja jiya Juma’a.

Da yake zantawa da manema labarai bayan ya ziyarci cibiyar Galaxy, gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da inganta hadin gwiwa da hukumar domin tabbatar da gudanar da harkokin mulki ta yanar gizo, inganta samar da kudaden shiga da kuma bunkasa fasahar sadarwa a jihar Jigawa.

A nasa bangaren, Manajan Darakta na Galaxy backbone, Farfesa Muhammad Abubakar, ya ce babban aikin hukumar shi ne gina manya-manyan ababen more rayuwa na zamani da hada kai da gwamnati. Ya yi nuni da cewa Galaxy ta himmatu wajen tabbatar da bunkasa fasahar zamani a Jigawa dama jihohi 36 a fadin tarayya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: