Mutane 16,000 ne zasu ci gajiyar tallafin rage radadi a karamar hakumar Malam Madori

0 323

Kwamatin rabon tallafin na jiha, karkashin jagorancin kwamishiniyar harkokin mata Hajiya Hadiza Abdulwahab ta bayyana haka lokacin kaddamar da rabon buhunan shinkafa, masara da taliya a Malam Madori.

Hadiza Abdulwahab tace gwamna Mallam umar Namadi, ya kaddamar da shirin domin tausayawa talakawa kan wahalhalun da aka shiga bayan cire tallafin ma fetur, ta hanyar rabon tallafi ga marayu, zawarawa, matasa da tsofaffi, masu rike da mukaman gargajiya, malamai da masu bukata ta musamman a kowace mazaba.

Ta bukaci mambobin kwamitocin su kasance masu gaskiya da adalci a matakan mazabu.

A nasa jawabin mashawarchin gwamna kan harkokin tsugunar da masana’antu Yakubu Usman Kacakama yace tsarin rabon ya kunshi, cewa kowacwe mazaba zata rabauta da buhun shinkafa 148, da katan din taliya 100 da buhun masara 275. Yace kansilan kowace mazaba shine shugaban kwamati a mataqkin mazaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: