Gwamnatin jihar Kano zata kashe akalla naira Miliyan 33 wajan bawa iyalan ma’aikatan jihar da suka mutu.

0 66

Gwamnatin jihar Kano zata kashe akalla naira Miliyan 33 wajan bawa iyalan ma’aikatan jihar da suka mutu wajan hidimtawa jihar Alawus Alawus.

Kwashinan yada labarai na jihar Malam Muhammad Garba shine ya bayyana hakan, inda yace bayan zaman majalissar zartarwa jihar da ya gudana a Africa House, gwamnatin jihar kano ta amince da biyan iyalan mamatan Alawus Alawus.

Kwamishinan ya kuma bayyana wadansu abubuwa da gwamanatin jihar ta amince da su, wadanda suka hada da biyan naira miliyan 80 a kowacce shekara wajan biyawa daliban da suke karatun likita na 1 da na 2, wadanda gwamnatin jihar ta tura su karatu a kasar Cyprus.

Haka zalika ya kara da cewa gwamantin jihar ta kafa wani kwamiti da zai bibiya karatun daliban tare da kawo bayani akan kudaden da gwamnatin jihar ta kashe da ya kai naira biliyan 1 da miliyan 1 a ranar 26 ga watan Nuwamba na 2020.

Ya kara da cewa a yunkurin da gwamantin jihar takeyi wajan habbaka fannin lafiya, gwamantin jihar ta amince da kashe naira miliyan 194 wajan sayawa ma,aikatan lafiyar jihar 17, 480 Unifoam.

Leave a Reply

%d bloggers like this: