Gwamnatin Najeriya ta ayyana Litinin, 3 ga watan Mayu a matsayin ranar hutu domin bikin zagayowar ranar ma’aikata ta duniya.

Ministan cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, wanda ya bayyana haka a madadin gwamnati, ya taya ma’aikata murnar zuwan ranar.

Ya kuma gode musu bisa irin hakuri da fahimta da kuma goyon bayan da suke bai wa tsare-tsaren gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari a kokarinta na ganin ta ciyar da kasar gaba ta fuskar ci gaban tattalin arziki da habaka al’umma.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: